2023: Ƙin yin katin zaɓe ke ƙara ta’azzara a tsakanin masu kaɗa ƙuri’a.

Ƙin zuwa domin mallakar katin jefa ƙuri’a yana haifar da damuwa tsakanin masu gudanar da zaɓe da masu fafutukar demokraɗiyya, tare da sauran masu fada aji a harkokin siyasa.

Yayin da babban zaɓen shekarar 2023 ke gabatowa, masu kada kuri’a ba sa son tsarin zaɓe, wani bincike da Aminiya ta gudanar ya bayyana haka.

Abubuwan da Jaridar ta Aminiya ta gano, ya nuna cewa fitowar masu kaɗa kuri’a a zaɓuka daban-daban, gami da zaɓen fitar da gwani kamar na kananan hukumomi, yawan masu kaɗa ƙuri’a na ƙara zabgewa.

class="has-text-align-justify">Hakan saya biyo bayan zaɓukan da aka gudanar da bayan babban zaɓen shekarar 2019 a wasu jihohi, inda waɗannan zaɓukan suka nuna yadda masu kaɗa kuri’a basu fito ba, kuma rashin fitowar tasu itace mafi muni tun da aka koma zaɓen shugaba ta demokradiyyar wato ta hanyar kaɗa kuri’a.

Masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen Najeriya da aka tattauna da su, waɗanda suka haɗa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ƙungiyoyin farar hula da masana kimiyyar siyasa, sun nuna tashin hankali kan haɗarin da ke tattare da wannan ƙin fitowar.

Muhimman dalilan da ke haifar da hauhawar rashin fitowar jama’a, a cewar masu ruwa da tsaki, sun haɗa da gazawar ƴan siyasa wajen cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen su, rashin shugabanci nagari, tsayar da’ yan takarar da ba a so, rashin tsaro, da sauran su.

Alkaluman hukumar INEC kan ci gaba da rijistar masu kaɗa ƙuri’a na ci gaba da bayyana cewa ƴan Najeriya nayin katin kaɗa ƙuri’ar a zahiri, amma masu ruwa da tsaki sun ce ƴan Najeriya nayin rajistan kawai don samun katin zaɓe domin wani amfani na daban, bawai don kaɗa zaɓe ba.
Duba da yadda tashe-tashen hankula ke haifar da ƙaura daga mazauna yankunansu, zaɓe a wasu sassan ƙasar na iya zama da wahala a gudanar.

Babban abin da a yanzu yake gaban INEC da jami’an tsaro shi ne yadda za a gudanar da zaɓen gwamna a ranar 6 ga Nuwamba a jihar Anambra. A makon da ya gabata, Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya ce gwamnatin tarayya na iya ayyana dokar ta-baci a jihar idan har ƙungiyar ƴan asalin yankin Biafra (IPOB) ta ci gaba da kai hare-hare. Kalaman Malami sun jawo babban suka da kace nace.

Ƙwararru kuma na fargabar cewa saboda rikice-rikicen da rasa muhalli da ayyukan ƴan bindiga ke haddasawa a jihohin Zamfara, Sakkwato, Kaduna, Katsina da Neja, akwai ƙarancin fatan gudanar da zaɓe a yankunan karkara da dama na jihohin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *