Da ‘dumi ‘dumi Ganduje ya aminta da kwace Jam’iyar APC da kotu tayi a hannunsa.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya roki ‘yan APCn bangaren sa su dauki hakuri da dangana tunda kotu tayi watsi da su kowa yayi biyayya.

Majiyarmu ta premium time na Cewa A ganawa da Ganduje yayi da jagorancin Jam’iyar APC bangaren sa karkashin shugabancin Abdullahi Abbas, ya ce zage-zage da kai ruwa rana ba zai sa a samu abinda ake so ba.

Kowa ya maida wukar a yi biyayya ga umarnin Kotu. Mu mutane ne masu da’a Kowa ya kwantar da hankalin sa.

Sai

dai kuma ganduje bau fadi ko bangaren nasa za su daukaka kara ba Bai Kuma Tabbatar da Cewa bangaren nasa ko zaiyi biyya ga bangaren Shekarau ba.

Idan ba a manta ba sau biyu kotu na yin watsi da zaben APCn bangaren gwamna Ganduje A cikin Nuwamba, kotu ta umarci su ganduje su baiwa bangaren Shekarau naira Miliyan 1 na bata masu lokaci da suka yi a kotu.

Mun buga labarin yadda wasu da ake zargin yan takifen bangaren Abdullahi Abbas ne suka cinna wa ginin APCn bangaren Shekarau wuta a Kano.

Sai dai ba ma yan jam’iyyar ba, yan gari wato mazauna unguwan suka fatattaki wadannan yan baranda.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu daga cikin wadanda ake zargin sune suka aikata wannan abu.

Siyasar jihar Kano na ci gaba da kicimewa musamman jam’iyyar APC ganin yadda ta rabu gida biyu a jihar.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba domin an gano akwai wasu yan bangaren Ganduje dake sakawa a boye suna yin rajista da APCn bangaren Shekarau.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *