A daidai Lokacin da Borno ke fama da Matsalar ta’addanci Gwamna Zullum ya Kori mutun dubu saba’in 70,000 daga aiki.

A daidai Lokacin da jihar Borno ke cigaba da fama da Matsalar ta’addancin Boko Haram muke samun rahoto na cewa Gwamnan Jihar borno Farfesa Babagana Umara zullum ya Kori ma’aikatan gwamnati a kalla sama da mutum dubu saba’in 70,000 a yunkurin sa na tantance ma’aikatan Gaskiya da naga bogi yawancin korar ma’aikatan Gwamnatin ta shafi malaman Makarantun firamari dana sakandiri matakin jiha dana kananan hukumomi ya Kuma shafi ma’aikatan aikin gona dana lafiya.

MIKIYA ta tattaro tare da kokarin jin ta bakin wata malamar Makarantar firamari daga karamar hukumar jere wacce ta bukaci mu sakaye sunanta Sakamakon wani dalili malamar Makarantar ta bayyana mana Cewa ita malamar Makarantar firamari ce ta Kuma ce Yanzu wattani goma kenan da aka dakatar dasu ba tare da an cigaba da biyansu albashin su ba, albashin nata da ya kai kimanin naira dubu ashirin da takwas N28,000 ta Kuma bayyana mana cewa ‘yan uwan aikinta da aka Kora albashin su ya ha’da da masu daukar N10,000 N11,000 N15,000 da Kuma masu kwalin NCE dake daukar albashin naira dubu Arba’in N40,000.

Malamar

Makarantar ta ce a iya karamar hukumar jere sama da mutum dubu ‘daya aka Kora a bangaren masu koyarwar matakin firamari da wasu bangarori na Ma’aikata Har’ila Yau Kuma ma’aikatan dake koyarwar a matakin sakandiri Suma an Kori sama da mutum dubu daya a ko wacce Karamar hukuma dake Jihar Borno.

Jihar borno Mai dauke da kananan hukumomi ashirin da bakwai 27 an Kori ma’aikata na matakin firamari sama da mutun dubu daya a ko wacce karamar hukuma dake Jihar Borno haka Kuma ma’aikata na matakin sakandiri anyi ittifakin Cewa kawo yanzu sama da mutun dubu Arba’in 40,000 aka Kora wanda yanzu Haka basu karbar albashi.

Gwamnatin jihar borno ta tabbatar da Cewa ta dakatar da ma’aikatan ne a wani salo na kokarinta na tantance ma’aikatan domin tabbatar da ma’aikatan Gaskiya dana bogi da Kuma bawa wa’yanda Basu da Cikakken ilimin koyarwa Sabon horo Zuwa matakin Ilimi Mai nagarta.

Masu Bincike a matakin duniya na cewa tantance ma’aikata ta Hanyar dakatar dasu ba tare da biyan su albashi ba na iya kawo wata barazana ga Lamarin tsaro musamman jihar Borno Dake fama da Matsalar ta’addancin Boko Haram na tsawon Shekaru goma Sha biyu wanda yayi sanadiyar Mutuwar sama da mutun dubu talatin da Shida 36,000 yayinda ya raba mutun Milyan biyu da dubu dari bakwai 2.7m da muhallin su bisa lissafin majalisar ‘dinkin duniya U.N.

Bincike ya nuna tare da tabbatarwa cewa Matsalar Rashin aikin yi ne Kan gaba-gaba wajen jefa matasa shiga harkokin ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *