A Gwamnati na Talakawan Nageriya Milyan takwas ke Samun tallafin duk wata, Haka Kuma kawo yanzu mun raba Bilyan dari uku 300bn ga manoma ~Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu ranar Talata a Abuja, yace a ci gaba da kokarin an rage talauci a Ƙasar an cigaba da kara adadin talakawa da gidaje Marasa galihu zuwa Miliyan Daya da Dubu Dari Shida, wanda ya kunshi sama da mutane Miliyan Takwas, wanda a halin yanzu suke cin Moriyar shirin bada Tallafin kudi kyauta, a yayin kuma da aka raba Biliyan Dari Uku ga Manoma.

Da yake magana ta Na’urar Sadarwa a Gurin taron shekara shekara karo na Goma sha Hudu a taron Masana da kwararru a harkan Banki da lissafi na Najeriya, Shugaban kasa yace, Kundin wallafa Sunayen Talakawa Ƴan-Nijeriya Nada Sunayen Mutane Miliyan Talatin da Biyu da Dubu dari Shida, daga cikin Magidanta Talakawa Miliyan Bakwai da aka zakulo, Shugaban ya miƙa rokon sa ga Masu harkokin Banki da su taka rawa sosai don inganta hanyoyin samun abin masarufi.

“Daga Cikin wannan Numba, gidajen Talakawa Miliyan Daya da Dubu Dari Shida, da suka kunshi sama da daidai kun mutane sama da Miliyan Takwas, yanzu suna cin gajiyar shirin tallafin kudi, wanda ake biyan Naira Dubu Goma duk bayan watanni 2 garesu,” Cewar Shugaban.

Shugaba Buhari, yace Shirin bada tallafi na Ƙasa, shirin mafi girma a Kasashe dake yankin Sahara kuma daya cikin Manyan shirin irin sa a Duniya.

Bisa ga Shugaban,” wasu cikin shirye shirye da mukeyi don bunƙasa kasuwancin Noma a Najeriya ciki harda shirin bada rancen Noman Shinkafa, Anchor Borrowers, wanda tanan ne Babban Bankin Kasa na CBN ya bada rancen sama da Naira Biliyan Dari Uku, ga ƙananan Manoma sama da Miliyan Uku da Dubu Dari Daya, ga Manoman kayan Gona daban daban daya hada da Shinkafa, Alkama, Masara, Auduga, Rogo, Kiwon Kaji, waken Suya, Gyada, Kiwon Kifi, wanda ya samar da filayen Noma sama da Hekta Miliyan Uku da Dubu Dari Takwas.

“Kundin bayanan mu ya nuna cewa kaso Tamanin cikin Dari na Shinkafa da ake amfani dashi a Najeriya a nan gida ake Nomawa.

Don kara karfafa da samar wa Ƴan-Nijeriya karin dama, Shugaba Buhari yace, a shekarar data gabata, ya amince da kafa kamfani InfraCo Plc, wanda na kai matakin kasa da kasa gurin Samar da cigaba, wanda kachokan ya maida hankalin sa a Najeriya, da samar da bashi da fara aiki da jarin dayakai Naira Biliyan Goma sha biyar, wanda masu samar da kuɗaɗen gudanar da Manyan aiyuka suka tanadar.

“Cikin watan Afrilu 2021, aka kaddamar da shirin Samar da Lantarki ta Hasken Rana, da zummar samar da cibiyoyin Lantarki wanda zai Samar da Lantarki ga Gidaje miliyan Biyar. A cikin watan Biyar 2021, Hukumar samar da Lantarki a karkara ta sanar da shirin rarraba Na’urar Samar da Lantarki ta Hasken Rana wa Cibiyoyin Lafiya daga Tushe Dari Biyu, da Makarantun Sakandaren Gwamnatin Tarayya guda 104 a daukacin kasa baki daya.

“A karkashin Shirin Asusun Samar da Gidaje wa Iyali, shirin Gwamnatin Tarayya na Samar da gidaje masu Rahusa, sama da hekta Miliyan Biyu na filaye an badasu tare da takardun su, wa Jihohi 24 ta yadda zai iya Samar da ƙusan Sabbin Gidaje Dubu Sittin da Biyar.

Wanda Babban Bankin ƙasa CBN yana Samar da kudin Naira Biliyan Dari Biyu don sayen kayan aiki, wanda Gwamnatin Tarayya ke tsayawa tsakani,” inji Shugaban.

Shugaban kasa, ya sake tabbatar da cewa, taken taron, ” Farfado da Tattalin Arziki, Hadaka, da kawo sauyi: Rawan da Banki da harkokin kudi zai taka” take ne mafi Dacewa, sakamakon yadda Duniya ta ƙaɗu daga Cutar Korona.

“Na injina wa Makarantar dama daukacin Bankuna da kamfanonin hada Hadar kuɗaɗe, kan yadda suka zage dantse Gurin tattaunawa a zahirance don Farfado da tattalin arziki, da gyara a Ƙasar, daga nan Najeriya zuwa Nahiyar Afirka kamar yadda taken taron naku ya kuntsa.

“Ina yabawa wa kamfanonin hada Hadar kuɗaɗe kan aiki Sakai da taimako don tabbatar da an samu karin dabaru Samar da kudi a Najeriya, musamman abu mafi Muhimmanci, rawar da Bankuna suka taka Gurin renon tattalin arzikin Kasar.

Ya kara da cewa “Ina da Ƙwarin gwiwa cewa, wadan da zasu yi fashin baki da aka zakulo su cikin Nutsuwa, don bada tasu Gudumowa a Gurin taron zasu kara wayar da kai sosai wanda zai taimaka wa daidaikun mutane da Ƴan kasuwa da Gwamnatoci a dukkan matakai don suyi duk wata gyara data dace da Daukan matakin daya kamata Gurin dunkulewar mu guri guda da dai dai ta Al’amura da sanya Najeriya a turba daya cewa don kai Kasar matsayin Manyan Kasashen Duniya masu karfin tattalin arziki.

Shugaban yace Rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa ya nunar da cewa, An samu haɓaka kayan da ake bugawa a Najeriya da kaso 5.01 cikin dari a cikin watanni uku na farkon shekarar 2021; wanda Shine haɓaka na farko tun bayan watanni kukun karshen Shekarar 2014.

“wannan labarin ne na farin ciki kuma haka ya nuna cewa kokarin da Gwamnatin nan keyi don sake kafa turban tattalin arziki bukata na biya,” yace, ya bukaci Bankuna da Cibiyoyin hada hadan kudade suyi amfani da damarmaki dake akwai kan kasuwanci Gurin haɓaka tattalin arziki.

Shugaba Buhari yayi roko ga cibiyoyin hada Hadar kuɗaɗe su taka rawa daya dace Gurin tabbatar da ƙananan da matsakaitan Ƴan kasuwa a Najeriya sun sanya su kan abinda ya dace, ta hanyar bada tallafi da aiwatar da dukkan yarjejeniyar da aka kulla.”

” Ba shakka babu wani lokaci dake da Muhimmanci na bukatar tallafin kudi daya wuce wannan lokaci, Muna Bukatar ku, Bankuna suke da Daraja da zasu jagoranci kirkiro da samar da Sabbin dabarun fasahohin zamani, da hawa turban samar da kudi ga Manyan aiyuka da zai sauya akalar tattalin arziki wanda ake tsammani amfana daga Yarjejeniyar,” Shugaban kasa ya nunar da hakan.

Yace, Sabbin sauye fasahohin zamani suma suna da Imfani a kasuwanci da zamani ke kai, ya lura cewa da yawan hada-hadar kudi da akeyi yanzu suna yiwuwa ne a yanar Gizo wanda yazo Yanar Gizo.

“a ci gaba da zuwa Mataki na gaba kan fasahar Sadarwan zamani, dole mu mara baya ga dukkan damar maki yayin kuma da zamu kiyaye Muhimman kura kurai, alal misali bada kariya ga bayanai yanzu ya zamo muhimmin abu don samawa masu Imfani da dasu tsaro a guraben dake a yanar Gizo.”

Shugaban kasa Buhari, yace Annobar Cutar Korona ta sauya komi a duniya, tun daga Mu’amala, gudanar da aiki, Sadarwa, dama yanayin gudanar da Rayuwa, ya shaida cewa Annobar ta kuma jawo Sabbin damaki wanda ya taimaka Gurin sake fasali ga tattalin arziki a fannin Sauyin fasahar zamani, tafiyar da kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, kashe kudade, tsaro, yanayin aikin sayar da magani a nan gaba, yadda ake Ƙere Ƙere, sanar da sufurin ka yaki.

“kamar yadda Muna dubi kan illolin Annobar anan gaba, akwai damar maki masu tarin yawa da muke dasu. Kamar yadda zamu iya sani dukkan mu, shirin tafiyar da kasuwanci kyauta tsakanin kasashen Afirka, wanda Najeriya tana daga ciki, ba dama ce kawai da haɓaka kasuwanci ba, dama ce ta haɓaka kasuwanci a Afirka.

“Ya kunshi damar maki sosai ga Ɗunbin matasan mu, Mata, kamfanonin kirkire kirkire, fassara kasuwanci zamani, hada hadan kuɗaɗe, tsarin kasuwancin Noma, kasuwanci, masana’antu, Ilmi, dama kuma dukkan abinda ya shafi dukkan harkan Kasuwanci kamar yadda Ƴan-Nijeriya zasu samu dama na sama da Naira Biliyan Daya da Miliyan Dari Uku, na kasuwancin abinda sarrafa wa, inji shugaban.

Shugaban kasa ya yabawa Babban Bankin Najeriya CBN, wanda ke aiki tare da hadin gwiwan Sauran Bankuna, don samar da kudade ga Matasa Ƴan-Nijeriya a fannoni dinke dinke, harkan Fina finai, wakoki, da fasahar Sadarwa ta zamani, ta hanyar kafa asusun ma’aikatar kirkire kirkire.

Cikin sakon fatan Alkhairi, Shugaban Ƙasar Rwanda Paul Kagame, yace fito da Sabbin fasahar a Fannin banki, da bada fifiko kan Sabbin abubuwan zamani, zai kara inganta hanyar Samar da kudade.

“Bangaren Banki zai iya yin jagoranci akan hanyar hadewa guri guda, harkan banki ta ta’allaka ne akan aminta,” a Cewar sa.

Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN Godwin Emefiele, yace Bangaren kula da harkokin Bankuna yana aiki tare da Sauran Bankuna don tsallake kalubalen da Korona ta kawo, wanda ya kunshi rage kudin ruwa (riba) kan bashuka, kara yawan lokacin biyan bashi, da kara Samar da bashin Naira Tiriliyan uku a fannoni masu zaman kansu.

Ya kara da cewa “Muna sa ran cewa, hawa hawan farashi zai daidaita a daidai lokacin da muke tunkarar lokacin girbi,” ya bada tabbacin cewa Bankuna basa fuskantar wata barazana.

Ya ce, kudin aiwatar da Manyan aiyukan cigaba Naira Tiriliyan Goma sha Biyar, za’a kaddamar dashi a watan Oktoba, 2021, yayin da Sabbin hanyoyi kamar Nigeria/International Financial zai samar da mashiga ta jari da kasuwanci, kuma harkokin kudade na fasahar zamani zai bunƙasa.

Femi Adesina:
Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a.
14th ga watan Satumba, 2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *