A Jihar Kano mun hana wankan tare na maza da mata a wuraren shakatawa Swimming pool. ~Ganduje

Gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin Dr Abdullah ganduje ta Hana maza da matan a jihar Kano wankan iyo ninkaya Swimming pool) a tare yadda gwamnati ta yi watsi da wankan amatsayin aika-aika a kwanakin baya gwamnatin jihar Kano ta kafa dokar da za ta hana maza da mata su kasance cikin tafkin ruwa daya Wannan ci gaban ya samu goyon bayan Task Force of Tourism Development Levy, da kuma goyon bayan gwamnati a wani yunkuri na dawo da zaman lafiya a cikin al’umma.

A

kokarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya da tsafta a tsakanin al’umma, gwamnatin jihar Kano ta haramtawa maza da mata yin iyo a wurin wanka daya, shan shisha, da shigar yara otal. Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an aiwatar da wadannan dokokin ne a karkashin Hukumar Task Force of Tourism Development Levy.
Shugaban kwamitin, Baffa Dan-Agundi, ya bayyana cewa, wadannan dokokin sun biyo bayan ganawar da suka yi da masu otal otal.

Sahara Reporters ta kara da cewa Dan-agundi ya bayyana haka ne bayan wani taro da masu gidajen otel da gidajen cin abinci da wuraren taron domin sanar da su sabon ci gaban da aka samu.
Kwamitin ya sanar da su wani sabon harajin da gwamnatin jihar ta yi wanda zai taimaka wajen tsaftace wuraren sana’o’insu da nufin kaucewa ayyukan karuwanci a jihar.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *