A Jos direban keke Napep ya komawa da fasinja dubu dari biyar N500,000 da ya manta shima Sarkin musilmai ya bashi kyautar dubu dari biyar N500,000.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya karrama wani mai tukin keke Napep mai suna Akilu Ahmad, Sakamakon ya dawo da kudi naira 500,000 da wani fasinja ya manta a keken sa a garin Jos, jihar Filato.

direban babur din mai shekaru 40 ya gano tare da mikawa wani fasinja jakar da ya bace dauke da tsabar kudi N500,000 ga wani fasinja a Jos, Jihar Filato, a ranar 14 ga Oktoba.

Mai martaba Sarkin Wase, Sambo Haruna ne ya gabatar da kudi da kuma yabo ga Malam Ahmad a yayin wani kwaryakwaryan biki da aka gudanar a dakin taro na babban masallacin Jos a ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoba.

Sarkin

Musulmi wanda Sarki Sambo ya wakilta ya ce mahayin Keke Napep ‘din ya baje kolin hakikanin koyarwar addinin Musulunci.

“Ya kamata a tunatar da mutane cewa a ko da yaushe akwai lada ga aikata alheri. Muna alfahari da wannan matashin da ya nuna koyarwar addinin Musulunci, da kuma matasa a Filato zuwa ga kyakkyawar fahimta,” inji shi.

Sarki Sambo wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Filato ya ce Sarkin Musulmi ya umarce shi da ya gano ko da gaske ne mutumin ya gano ya mayar da kudin.
Ya ce da ya gano cewa gaskiya ne, Sarkin ya aika daidai da Naira 500,000 a bai wa Malam Akilu a matsayin ladan aikin alheri.

Shima Mai Martaba Sarkin Kanam Muhammad Babangida Mua’zu a lokacin da yake gabatar da kudin, ya ce abin da Malam Akilu ya yi ya cancanci a yi koyi da dukkan musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *