A kokarinta na gujewa kamu daga jami’an tsaro, tsohuwar ministar sufurin jiragen sama Stella Oduah ta mika kanta ga kotun Abuja domin amsa tuhuma bisa almundahanar Naita biliyan 7.9bn.

A kokarinta na gujewa umarnin kamu, tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Mrs Stella Adaeze Oduah, ta isa babbar kotun tarayya dake Abuja, domin gurfana bisa tuhumar da ake yi mata na laifin almundahanar naira biliyan 7.9 da gwamnatin tarayya ta shigar a gaban kotun.

A baya dai an dage shari’ar da har sau biyar saboda rashin zuwanta kotu da kuma hutun.

Mai shari’a Inyang Eden Ekwo a ranar 12 ga watan Yuli ya yi barazanar bayar da sammacin kama Misis Stella Oduah idan har ta kasa gabatar da kanta a gaban kuliya a ranar 19 ga watan Oktoba da aka dage sauraron karar, wadda daga baya ta koma hutu.

An

yi barazanar kama ta ne biyo bayan rashin bayyanar ta da rashin girmama shari’a da kotu a ranar 12 ga watan Yuli ba tare da wani bayani daga bangarenta ba.

Yunkurin da aka yi na kama ta a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba, kan shari’ar satar kudi, ya ci tura ne sakamakon hutun Eid el Maulud da gwamnatin tarayya ta ayyana na murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (s.a.w).

Mrs Oduah, wacce a yanzu sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta Arewa a majalisar dattawa ta kasa, ta isa kotu da misalin karfe 8 na safe domin fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 25, tare da wasu hudu.

Sanata Oduah dai ta samu rakiyar wasu jami’an tsaro, abokai da kuma abokan siyasa a gaban kotu.

A daidai lokacin da ake wannan rahoto, Sanatan na tattaunawa ne a minti na karshe kafin a gurfanar da ita da lauyanta kan mataki na gaba.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na zargin Mrs Oduah da karkatar da kudaden gwamnati na N7.9B a lokacin da take rike da mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Gloria Odita, Nwosu Emmanuel Nnamdi, Chukwuma Irene Chinyere, Global Offshore, da Marine Limited, Tip Top Global Resources Limited, Crystal Television Limited, Sobora International Limited, da wani kamfanin gine-gine na kasar waje.

Ana tuhumar su da laifin hada baki da halasta kudaden haram, da kuma rike asusun ajiyar banki da ba a san sunansu ba.

Lauyan mai shigar da kara, Dokta Hassan Liman, Babban Lauyan Najeriya, SAN, ya isa kotu tare da wasu lauyoyi kusan 12 don gabatar da karar da gwamnati ke yi kan wadanda ake kara.

Tun da farko Liman ya ce an jera shaidu 32 don ba da shaida kan Sanata Oduah da wasu mutane 8 da nufin tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *