A matsayin sa na shugaban kwamitin bankuna Sanata Uba sani yace zai yi aiki da tsare tsare domin gyara tattalin Arzikin Nageriya.

Sanata Uba sani yayi wannan magana ne a cikin sakon sa na godiya da ya aikewa Jaridar Goardian, bisa karramashi da Lambar yabo amatsayin jajirtaccen ‘dan majalisar dattijan na Farko a majalisar dattijan Nageriya ta tara 9 Sanatan ya mika sa Sakon godiya ne ga Jaridar bisa Zaben nasa da wannan mataki na cigaba da tsayawa ga Al’ummarsa.

A Sakon nasa Sanatan na Cewa Ina so in nuna matukar godiyata da Farin ciki ga sashin gudanar wa da Ma’aikatan wannan Jarida ta Guardian Najeriya, da suka amince da ni a matsayin “Sanata mafi fice a karon farko a Majalisar Dokoki ta Kasa ta Tara 9”.

Hakika

wannan kyauta tana ‘daya daga Cikin kyautar da nake Matukar ƙauna, Guardian ta Kasance Mai ma’ana tare da kyawawa ayyuka da sadaukar da kai ga kare dimokuradiyya, hakkoki da ‘yanci a duk Najeriya. duk da manyan kalubale Amma kuna cigaba da haskawa inji Sanatan

Sanatan yace a daidai wannan Lokaci wata dama Cewa ‘dauke da kalubalanta Mai nuni da Cewa na kara karfin gwiwa domin aiwatar da ayyuka mafi kyau a gaba, na kuma himmatu tare da ci gaba da daukar nauyin kudrai masu tasiri, Ba zan taba yin kasa a gwiwa ba wajen gabatar da kudiri kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa. Mazabana za su ci gaba da jin daɗin wakilci mai kyau nawa.

Zan yi aiki tare da abokan aiki na na Majalisar Dokoki ta kasa don tsara ingantattun tsare-tsaren doka domin magance kalubalen tattalin arzikinmu Inji Sanatan.

Sanatan ya Kara da Cewa Yana godiya da ya Zama na Daya tilo wanda ya cancanci wannan karramawa.

Sanata Uba sani dai shine Sanata mafi Kai Kudrai kala-kala a duk Tarihin Sanatocin da suka wakilci jihar kaduna ta tsakiya tun dawowar mulkin dimokuradiyya a Nageriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *