A Shirye Nake Da Na Sadaukar Da Raina Domin Kasata Nijeriya, ~ Cewar Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar bikin dimokiradiyya ta bana, inda ya yi karin haske kan wasu muhimman ayyukan gwamnatoci da kalubalen tsaro da sauransu.

A yayin jawabin shugaban a yau da safe ya sha alwashin kare wanzuwar Nijeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sannan kuma ya yi wasici da zaben gaskiya da adalci a 2023.

“Ranar da na shiga rundunar Sojan Nijeriya na shirya sadaukar da raina saboda Nijeriya.

Haka

zalika har yanzu a shirye na ke in sadaukar da raina domin Nijeriya.

A matsayina na shugabanku, na ci gaba da jajircewa wajan kare wanzuwar Nijeriya.” Inji shugaban.

Daga: Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *