A soke lefe da kayan daƙi, akai mace tsinkin ragin ta gidanta, domin yan mata sunyi yawa yanzu — Fauziyya D Sulaiman.

Fauziyya D Sulaiman

Al’adar lefe da kuma siyowa ƴan mata kayan ɗaki ya zamarwa iyaye marasa shi ƙarfen ƙafa a wannan zamanin da muke ciki wanda yanayin tattalin arziki ya shiga wani yanayi na la-ila-ha-ula-i.

Duba da irin wannan yana yi ne, yakai hankalin ƴar gwagwarmayar nan mai suna Fauziyya D Sulaiman kan lamarin, tunda ta kasance mai gudanar da wata gidauniya mai bada tallafi ga marasa ƙarfi wacce ake wa kirari da “Creative Helping Needy Initiative“.

class="has-text-align-justify">A cikin wani Faifan bidiyo data ɗaura a shafinta na Instagram, Malama Fauziyya tayi wani bayani mai sosa rai, wanda take ganin ya kamata iyayen mu Hausawa suyi la’akari dashi domin tsaida wannan al’ada ta lefe da kayan daƙi.

Fauziyya D Sulaiman ta ƙara da cewa:

Halin da muke ciki na jarabawar Ubangiji, takai halin da iyayen mu, basa iya yiwa ƴaƴan su mata kayan ɗaki, kasancewar ina da gogewa wajen taimakawa al’umma, ya kasance babu ranar da garin Allah zai waye ba tare da anzo min roƙo na kayan ɗaki da za’ai wa yarinya ba“. Inji ta.

Ta ƙara da cewa:

Akwai mahaifiyar da tazo min ta ke faɗamin

Sau huɗu ana kawo kayan yarinyar ta, ana ɗaga bikin saboda basu da yadda zasuyi suyi kayan ɗaki, tsawon shekaru uku zuwa huɗu.

Fauziyya D Sulaiman taci gaba da cewa:

Akwai wacce tacemin, ita bazawara ce, kuma sau uku ana kawo kayan auren ta, to amma saboda batada halin kayan daƙi, abin na lalacewa. Hartakai, wasu mazan ma na ƙoƙarin lalata da ita saboda sun kawo kuɗin aure“.

Fauziyya D Sulaiman

Fauziyya D Sulaiman tace, tunda ba al’adar mu bace namiji da zai auri mace yin kayan ɗaki, kamar wasu ƙasashen, to mu koma yadda addini ya tanadar.

Inda tace, akai mace da abubuwan buƙata na rayuwa da suka zama tilas ba ko kuma akaita tsinkin ragin ta.

Domin sauraran cikakken maganar kalli bidiyon anan:


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *