A watan Disamba mai zuwa zamu fara kunna maku wutar lantarkin Zungeru ~Cewar Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa, nanda watan Disambar bana, za’a kammala aikin tasoshin samar da wutar lantarki ta Zangeru da Kashimbila.

Ministan Lantarki na ƙasa Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka ga kwamitin majalisar Dattawa mai kula da bangaren wutar lantarki, a yayin da ya gurfana gaban kwamitin domin kare kasafin kudin ma’aikatar sa.

A cewar Ministan samar da lantarki, a tashar samar da lantarki ta Kashimbila wacce zata rinka samar da Mega wat 40 kuma zata fara aiki ne a cikin watan Disamba.

A

cewar sa tuni Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biya bashin da ƴan Kwangila suke binta har Naira biliyan 10.

Sai dai kuma Ministan yayi gargadin cewa fara aikin tashar ka iya gamuwa da tazgaro a cikin watan na Disamba sakamakon matsaloli na tsaro a jihar Niger.
Amma koma dai mene a watan Disambar wadannan tashoshi zasu fara aiki a cewar sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *