A yanzu kam ko ‘yan Arewa sai sun mika sakon godiya ga majalisa idan suka tsige Buhari ~Cewar Aisha Yusufu.

‘Yar rajin kare hakkin bil’adama, Aisha Yesufu, ta ce lokaci ya yi da majalisar dokokin kasar nan za ta tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Yesufu, Wacce itace wacce ta jagoranci kungiyar BringBackOurGirls Movement, tana mayar da martani ne kan sabon lamarin da yake faruwa na sace-sacen mutane da kashe-kashe a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ta rubuta cewa, “Tun da naji labarin harin da kashe-kashen da aka yi a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ban iya yin komai ba, kuma a Lokacin Ina da Ayyuka da yawa da zan yi Yesufu ta rubuta a shafin Twitter tana Mai Cewa

“Me

Majalisar Dokoki ta Kasa take yi? A tsige Buhari! Kawai ko Jama’ar Arewa za su gode muku! Ba ku da lafiya domin sun gaji da marasa zuciya a matsayin babban kwamandan. Kasa

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kuma mayar da martani kan harin da ‘yan bindiga suka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka yi garkuwa da mutane da dama a ranar Lahadi.

Gwamnan yayi magana ne a ranar Litinin ta bakin kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar, Samuel Aruwan.

Ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu matafiya yayin harin.

A wata sanarwa da Aruwan ya fitar ya ce an kubutar da goma sha daya daga cikin mutanen da aka sace.

Ya kuma ce wanda aka kashe yayin harin shi ne shugaban makarantar Famaks British School kuma tsohon Dan takarar gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Sagir Hamidu.

Titin Abuja zuwa Kaduna wuri ne da ake yawan kai hare-haren ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *