ABIN MAMAKI: Sadio Mane duk da kasancewarsa multi-biloniya amma da fashashshiyar waya ya ke amfani

Sadio Mane Duk Da Kasancewarsa Multi-Biloniya Amma Da Fashashshiyar Waya Ya Ke Amfani

Shahararren ɗan ƙwallon duniya ɗan asalin ƙasar Senegal da ke yammacin Afrika Sadio Mane wanda duk sati ya ke karɓar albashi mai tsoka, an sha ganinsa a wurare da yawa yana amfani da waya a fashe, Da ake tambayarsa dalilin daya saka ba zai siyi sabuwar waya ba a wata tattaunawa. Sai ya ce:

“Zan iya siyan wayoyi sababbi guda dubu, motoci ferrari 10, jiragen hawa guda 2 da agogon zinare, amma me yasa zan buƙaci duk waɗannan?

Na

ga talauci da idona, shin ba zan ɗauki darasi ba? Gara na gina makarantu al’umma su samu ilmi, akwai loƙacin a baya na yi ƙwallo ko takalmi babu, bani da kayayyakin sawa masu kyawu, Bani da abincin da zan ci. Amma a yau ina da kuɗaɗe masu yawa, dan haka gwada na kashe su tare da mutanena maimaikon yin riya da alfahari”

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *