Account ‘din bogi a Facebook Mai Mutuwar Karya Namiji da suna Ayshet Mohammed Nasara ya ja Hankali.

Kawo yanzu mun gudanar da Bincike Mai zurfi Kan wani account na bogi a Facebook Wanda ya ja hankulan masu ta’amali da shafukan sada zumintar zamani account ‘din mai suna Ayshet Mohammed Nasara, me anfani da wannan account ya yi karyar mutuwa ta hanyar yaudara Mai ‘dauke da jan hankulan jama’a musamman masu raunin zuciya domin tausayawa, acikin kundin bayyana kanka na Facebook Ayshat ta rubuta cewa tana Karatu a jami’ar bayero dake Kano Kuma tana Zama Abuja ita haifaffiyar garin gumel dake jihar jigawa ce, A Ranar talata 12/10/2021 da misalin karfe 08:39am aka rubuta sako da account din na bogi
Ana

Mai cewa Am Regret To Announce You That Jiya Rashin Lfy tawa Yatashi around 12 na Dare. Munje Asibiti. Result Din Shine Insha Allah Yau by 4 na Yamma Za’a Mini Tiyata.

Include Me In Your Prayers pls. Bye. Am going to Miss You!!!

Jim ka’dan Bayan haka Kuma a ranar dai ta talata 12/10/2021 da misalin karfe 09:08am aka sake rubutawa ana cewa Dan Allah Duk Wanda Nayiwa Laifi Ya Yafe mini. Ni Aisha Nasara, Na Yafewa Kowa Da Kowa.

A Tsorace Nake Wallahi. Ji Nake Kamar Mutuwa Zanyi Wallahi… Ku Yafe mini Dan Allah.

Har’ila yau A ranar dai ta talata bayan awanni wato da misalin karfe biyu da rabi 02:30pm sai labarin rasuwarta ya bayyana ya kuma kara’de shafukan sada zumintar zamani musamman na hausa, lamarin da ya sa jama’a da dama tausayawa a gare ta tare da addu’ar Neman rahamar Allah a gareta duda da sakon da ta wallafa a shafin ta ba tare da jumawa ba Kuma mutuwar ta bayyana.

Bincike…

Mohammed nasara wani babban mutun ne a garin gumel mun bincika Babu wannan sunan a gidansa Kuma ba ayi masa mutuwa anan kusa-kusa ba.

Da mukayi anfani da app, Mai suna Facebook fake account checker, sai ya nuna mana lambar da aka bude account din ansha bu’de account da ita ana rufewa har sau biyar Wanda a cikin account din akwai sunan mata dana maza Kuma ko wanne an rufe shi tun a baya saura daya kacal.

Hotunan da ake anfani dasu a account duk kansu a Facebook ake cire su a shafukan wasu ba ta6a ‘dora Sabon hoto Wanda ba ayi anfani dashi ba a Facebook.

Ba’a taba Dora Sabon hoto a kan account din ba sai idan wani ya dora daga baya sai a cire a saka a wañnan account Mai suna Ayshet Mohammed nasara.

Sama da mutun milyan biyu ne suka karanta labarin wannan rasuwa amma haryanzu ba’a iya samo ko da mutun ‘daya wanda zai ce ya santa a zahiri ba sai a Facebook.

Kawo yanzu kusan mutun biyar ne Suka bayyana cewa an so a damfara 419 da account din.

Babu Wanda ya taba magana ta hanyar Kiran waya da Ayshat Mohammed nasara sai dai Chat.

Dukda cewa labarin ya zama babban labari a cikin zukata jama’a Amma Cikin wa’yanda sukayi alhinin mutuwar wannan mai account din bogi haryanzu ba’a samu ko mutun ‘daya da ya bayyana ya ce ya santa ba,

Duba da cewa Mai wannan account ya bude account har sau biyar kuma da number ‘daya uku sunan maza biyu sunan mata Kuma daga baya duk an rufe su saura ‘daya. Lambar da ake anfani da ita domin bu’de account din namiji ne ke da mallakin ta hakan ya tabbatar Mana da cewa namiji ne ke bude account din domin yaudarar jama’a

Bincike ya nuna mana cewa ana bude account din ne domin cin mutunci ‘Yan siyasa da Kuma shirya damfara ta hanyoyi da dama, Yan jaridar hausa ne Suka baza labarin ba tare da bincike ba.

Sai a kiyaye da yada labari ayi bincike kafin wallafawa domin gudun jin kunya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *