Adawar Siyasa Shehu sani ya kulle Jama’arsa ga bayyana ra’ayoyin su a shafinsa na facebook.

Tsohon Sanatan kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya Sanata Shehu sani ya kulle bangaren bayyana ra’ayin Jama’a (Comment section) a shafin sa na Facebook tun bayan faduwarsa zabe a zaben 2019 Sanata uba sani shine ya tika shehu sani da Kasa a zaben daya gabata na 2019, bayan wannan Lokaci ne ‘yan adawa suka cigaba da sako Sanata Shehu sani a gaba Kan rashin samun nasara a zaben, lamarin da masu hasashe da bayyana ra’ayi yasa suke ganin cewa shehun ya kulle bangaren bayyana ra’ayoyin ne a kokarinsa na gujewa CeCe kucen Jama’a Sakamakon faduwarsa zaben, wasu Kuma na ganin rashin son jama’a ne yasa Sanatan kulle account din ba tare da barin kowa ya bayyana ra’ayinsa duba da cewa ko wanne ‘dan siyasa na jama’a ne Kuma ana bukatar ya kasance mai sanin darajar Dimokuradiyya ta hanyar bawa kowa ‘yancin fadin Albarkacin bakin sa.

class="wp-block-image size-full">

Shehu sani da yakasance ‘dan Jam’iyar APC kafin ya canja sheka zuwa Jam’iyar PRP biyo bayan faduwarsa zaben fidda gwani na cikin gida idan Baku manta ba dai Kafin zaben Shehu sani yasha cika baki tare da alwashin Samun nasara Kan abokin bugawarsa Sanata Uba Sani a zaben na 2019 a karkashin jam’iyar PRP.

Sanata Shehu sani wanda ya kwashe shekaru hudu cif-cif a majalisar dattijan Nageriya Yana wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, jama’a na ganin cewa babu wani abin azo a gani daya yi na aikin mazaba a yankinsa duba da yadda Sanata Uba sani yazo cikin shekaru biyu kacal Amma ya Kai cigaba Mai ‘dunbin tarin yawa a yankin na Kaduna ta tsakiya da jihar Kaduna dama Nageriya amatsayin sa na Sanata Kuma shugaban kwamitin inshora bankuna da sauran harkokin ku’di na majalisar dattijan Nageriya.

Kawo yanzu Sanatan uba sani ya Kai Kudrorin cigaban al’umma sama da guda Ashirin 20 cikin shekaru biyu 2, wanda tuni shugaban Muhammadu buhari ya saka hannu akan ‘daya daga cikin kudrin hakan ya bawa kudrin damar Zama doka a Nageriya, Bayan haka Sanatan ya kafa cibiyoyin koyon sana’o’i kala-kala tare da Samar da jari ga matasa domin samun damar dogaro da Kai hakan ya bawa sanatan damar samun Lambobin yabo kala-kala amatsayin gwarzon Sanatan taimakon Al’ummarsa a duk fa’din majalisar dattijan Nageriya.

A zaton Sanata Shehu sani na gaf da bude Sashin na bangaren bayyana ra’ayoyin jama’a a shafin sa na Facebook duba da cewa Lokacin zaben na 2023 na cigaba da karatowa Kuma zai fara neman tallafin jama’a Bayan bayyana ra’ayinsa tsayawa takarar Gwamna a jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *