AIKI NA KYAU: Yadda ‘yan sandan Zamfara suka kama ‘yan bindiga 69 da masu hada baki da su

A ranar Lahadi, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana yadda ta samu nasarar kama mutane 21 da ake zargin ‘yan bindiga ne da su ka addabi jihar tare da masu taimaka musu guda 69 duk a cikin watan Satumba.

SP Muhammed Shehu, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, inda yake lissafo tarin nasarorin da jami’an tsaro su ka samu a jihar.

Kamar yadda ya bayyana, sun halaka shu’uman ‘yan bindiga 5 da jami’an tsaro su ka bayyana su na nema ido rufe.

Ya

bayyana cewa: “Tun bayan gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya samar da sababin dabarun kawo karshen rashin tsaro a jihar, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun cigaba da bin hanyoyin kawo karshen ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane dake jihar.

“Sakamakon yadda jami’an tsaro su ka jajirce kuma su ka dage, an samu nasarori da dama don yanzu haka an halaka ‘yan bindiga sannan kuma hari, kashe-kashe da garkuwa da mutane duk sun rage a watan da ya gabata.

“Hanyoyin da gwamnan ya samar sun dakatar da ‘yan bindiga daga samun abinci, man fetur, magunguna har da sauran ababen bukatun su.

“Yanzu haka an dakata daga biyan su kudaden fansa duk sakamakon tsaron da gwamnan ya sa a jihar, yanzu haka babu hanyar sadarwa tsakanin ‘yan bindiga da masu ba su bayanai na musamman.”

Ya kara da bayyana yadda yanzu haka mutanen da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su suka zama ayyuka manya gare su don haka su ka dinga sakin su, bayan ‘yan sanda sun dage da neman su.

Tsaron da gwamnatin ta samar ya kara bunkasa tsaro a birane ta hanyar dakatar da ta’addanci irin garkuwa da mutane, fashi da makamai, kwacen motoci, balle gidaje da sauran su.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *