Alkalin Kotun Tarayya na Babban Kotun Abuja, Okeke, Ya Mutu

Mai shari’a Jude Okeke na Babban Kotun Tarayya ya mutu.

An rawaito cewa mamacin alkalin mai shekaru 64 ya mutu a Babban Asibitin kasa da ke Abuja.

Okeke ya kammala karatunsa a 1985, kuma ya kammala aikinsa na bautar kasa a shekarar 1986, kana ya zama lauya.

Ya rike mukamin shugaban kungiyar lauyoyin najeriya, reshen Abuja har zuwa lokacin da aka nada shi alkalin babbar kotun Birnin Tarayya a shekarar 2007.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *