Allah Ka Isar Mana — Datti Assalafy

Shahararren ɗan gwagwarmayar nan kuma masanin sirrin tsaro da kuma hada hadar yanar gizo-gizo wanda aka sani da Datti Assalafy yayi wani rubutu a shafin sa na kafar sadarwa ta Facebook, wanda ya bawa masoyan sa mamaki.

Datti Assalafy, wanda yake sananne kuma na gaba gaba a farfajiyar soyayyar Muhammadu Buhari, ya nuna ɓacin rai akan yadda abubuwa suke ta kacamewa a ƙasar nan, musamman ma tun lokacin da ƴan bindiga suka tare matafiya guda 42 da biyu suka banka musu huta, ciki kuwa harda ƙananan yara.

class="has-text-align-justify">Biyo bayan hakan ne, aka hango Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi Lagos ƙaddamar da littafin bayarabe Bisi Akande daya rubuta, maimakon yaje yayi ta’aziyya da ɗaukan matakin daya dace.

To sai dai daga baya, shugaban ya tura wata tawaga ta musamman wacce a cewar su, hakan anyi ne domin binciko dalilin da yake haddasa wannan matsala, domin shawo kanta na dindindin.

To da alama dai, wannan batu ya canja salo.

Domin kuwa, wasu na zargin anyi hakan ne kawai domin damuwa da mutane sukayi akan sai shi shugaban yaje.

Wasu kuwa cewa suke ai ba wani binciken da za’a yi, kawai an tura su suyi ta’aziyya ne, sanin cewa, yan Arewa mantuwa ne dasu. Da anyi hakan zasu manta.

Ga rubutun Malam Datti Assalafy:

“Ba a kyauta mana ba, an mana karya, an yaudare mu, an mayar damu saniyar ware, kuma an zalunce mu an tauye mana hakki
Allah Ka isar mana”
. Inji Datti.

To sai dai masu bibiyar sa, sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan batu:

Abubakar Idreth Abubakar cewa yayi:

“Wai kai dan Allah ka zaci bincike atura su ba gaisuwa ba?

ko atunanin ka za ayi adalci ne baya tsinannu maciya amanar ƙasa sun zagaye mai gaskiyan”.

Idris Hassan Idris nuna mamakin sa yayi akan wanann salo na rubutun Datti Assalafy, duba da yadda yake gwani a wajen nuna soyayyar sa, ga gwamnatin Muhammad Buhari.

“Anya kuwa ba Haking aka yiwa Datti Assalafiy ba domin kwana biyu ina gani wasu irin rubuce rubuce na suka gwamnatin mu anya kuwa Dattin dana sani ne?”.

Maryam Rabeeu Ukhti kuwa cewa tayi itama tana mamakin yadda Malam Datti Assalafy yake ƙoƙarin sauka daga kan motar shugaba Muhammadu Buhari:

“Laaa jamaa malam datti ya sauka daga motar baba buhari Allah yasa lokacin dakaso durga bakaji ciwo ba”.

Koma dai menene, mudai, fatanmu Allah ya kawo zaman lafiya ga ƙasar mu, sannan ya bawa shugabannin mu, daman ganin sunyi abinda zai taimakawa al’ummar da suka zaɓe su.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *