Amurka ta gano wani sirri: ‘Yan bindiga na hada kai da Boko Haram domin shirya sabon ta’addanci don ‘bata gwamnatin Buhari

Wani kwamitin kasar Amurka ya bankado yadda ‘yan ta’addar Boko Haram da ke aiki a Arewa maso Gabas ke hada kai da ‘yan bindiga da ke addabar al’ummomin Arewa maso Yamma don karbar kudin fansa daga gwamnatin Buhari da fararen hula.

Wannan na zuwa ne daga cikin rahoton wata jaridar Amurka mai suna The Wall Street Journal a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba.

Jaridar ta Amurka ta ba da rahoton cewa Amurka ba ta mai da hankali kan ‘yan bindiga a matsayin barazana kai tsaye ga muradun ta ba, sai dai, jami’ai na sa ido kan kwamandojin ‘yan ta’addan da ke hada kai da mayakan Boko Haram.

Rahoton

na Amurka zai iya karfafa kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na ayyana ‘yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda, duk da cewa ba su da wata manufar siyasa ko ta’allaka kansu da addini da suka bayyana.

Jami’an gwamnatin Najeriya sun ce gwamnati ba ta cikin gaggautar ayyana ‘yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda, amma ta umarci jami’an tsaro da su kara kaimin fatattakarsu a dazuzzuka da sauran maboyarsu.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *