An damke wata mata bisa zargin laifin damfarar wani matashi Milyan uku da sunan EFCC

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta damke wata mata mai suna Hajiya Hadiza Umar Abubakar bisa laifin damfarar wani mai neman aiki a hukamar ta EFCC Nuraddeen Abubakar kan kudi N3,000,000 ta hanyar yi masa alkawarin karya na samo masa aiki a EFCC. An kama wacce ake zargin ne a wani reshen bankin Guaranty Trust Bank (GTB), yayin da ta tura danta don yaciro mata kudi, ba tare da sanin cewa Hukumar ta EFCC tasa matakan Hana ciran kudi na Post No Debit (PND) adukkan asusunta ba. Bayan an Tsare danta a bankin ya sa ta bayyana sannan daga karshe Hukumar ta kama ta.

Tun

farko matar dai tace zata sama mawa Nuraddeen aikin ne kan zunzurutun kudi har N6million, wanda tayi ikirarin zata taimaka masa samun aikin a EFCC. Wanda tuni Mai neman aikin ya sanya N3million a cikin asusun matar a ranar 29 ga Oktoba, 2019, yayin da za a biya sauran bayan aikin ya tabbata wato idan ya karbi Wasikar Fara Aiki, wanda aka yi alkawarin za a kawo, makonni biyu daga ranar da akayi biyan farko. , A watan Nuwamba 7, 2019 azaman kwanan watan. A cikin takardar koken da ya aikawa hukumar ta EFCC, wanda lamarin ya rutsa da ita, wanda ya bayyana cewa ya sadu da wacce ake zargin ne, ta hannun danta, ya bayyana cewa bai samu wasikar daukar aikin EFCC din ba tswon watanni tara bayan biyan kudin da aka ba ta. Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da matar a gaban kuliya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *