An gano masana’antar hada-hadar sayarda jarirai a jihar Kano.

Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta gano wani gida da ake killace mata masu ciki kuma ake siyar da jarirai a jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan, Haruna Mohammed ya sanar da haka a jiya Alhamis a garin Awka dake jihar Anambara.

Kakakin ƴan sanda Mohammed ya ce sun kama mata har goma dake da hannu a wannan sana’a sannan sun kuma ƙwato jarirai biyar a wannan gida bayan wasu ƴan mata 3 da ka same su ɗauke da tsohon ciki suna gab da haihuwa inda daga bisani za’a kwashe ƴaƴan a biya su kuɗin su.

Ya

kuma ce rundunar ta ceto wasu ƙananan yara guda uku a ƙauyen Oba dake ƙaramar hukumar Idemili.

An gano gidan siyar da jariran ne a ƙauyen Oba dake Idemili ta Kudu. Bincike ya nuna cewa wata mata mai suna Uju Uba ce ke da gidan wanda ke kusa da asibitin koyarwa na jami’ar Nnamdi Azikiwe.

Rundunar ta kama waɗanda suka haɗa da Edna Nnadi mai shekaru 37, Ujunwa Nweke mai shekaru 25, Izuchukwu Uba mai shekara 24, Chinasa Ibeh mai ahekara 19, Peace Effiong Mai shekara 25, Gift Collins Mai shekara 20, Chimkaso Kingsley Mai shekara 25, Happiness Monday mai shekaru 18, Chioma Okonkwo mai shekara 25 da Uchechukwu Nwankwo, mai shekara 18. Mata biyar daga cikinsu na dauke da tsohon ciki.

Mohammed ya ce rundunar za ta kai yara ukun da jarirai biyar ɗin da ta ƙwace su daga gidan zuwa ma’aikatar kula da al’amuran mata da ƙananan yara na jihar.

Ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da yin farautar gidaje irin haka domin kamo ire-Iren mata haka da ke kasuwancin jarirai a jihar

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *