An hango hotunan fastar “Aisha Yesufu” da Mawaƙin gambara “Falz” domin tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023.

An hango ƴan gwagwarmayar ne a ƙarƙashin wata jam’iyya da take iƙirarin kare rajin ɗabbaka tafiyar harƙallar titi wato (Street Mobilisation Group).

Ita dai wannan ƙungiya, sun yi kira ne ga ƴan gwagwarmayar ne dasu fito domin canja fasalin ƙasar nan, duba da sune gaba gaba a jagorantar masu zanga-zangar nan da tayi ƙaurin suna ta Endsars.

To

sai dai abinda ba’a sani ba shine, da masaniyar mutanen akayi wannan hoto aka liƙa a tituna ko kuwa wasu ne suka gaba-gaɗi sukayi.

To ko menene dai, masana harkar siyasa suna cewa, lokaci ne zai nuna wanene ba wanene ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *