An nuna min marigayi Fasto TB Joshua na tiƙa rawa da Mala’iku a lahira a mafarki |– In ji Wani mabiyin sa

Wani dan ƙasan India mai suna V. Justin ya bayyana cewa ya ga hango babban faston cocin Synagogue SCOAN dake marigayi TB Joshua tare da mala’iku suna rawa a lahira.

Justin ya ce ya ga haka ne kwanaki kaɗan bayan rasuwar fasto Joshua a wani bidiyo da aka saka a shafin Facebook din shi marigayin ranar Laraba.

“Na yi wannan mafarki ranar 14 ga Yuni inda a cikin sa aka nuna min TB Joshua cikin farin ciki tare da mala’iku suna tika rawa a lahira

“A

mafarkin na ji murya na cewa annabi TB Joshua na tare da Allah kuma yana cikin farin ciki a Lahira.

“Ganin haka ya sa na yi gaggawar faɗi wa mutane cewa marigayi TB Joshua mutumin Allah ne kuma yana cikin zukatan mutane.

A ranar 5 ga Yuni ne TB Joshua ya rasu kwanaki kaɗan kafin ya cika shekaru 58 a duniya.

Mabiyansa a Najeriya da kasashen wajen kasar nan sun yi jimami da alhinin rasuwarsa.

Marigayi TB Joshua ya shahara matuka wajen aikin yin wa’azi da kuma warkar da marasa lafiya ta hanyar addu’o’i a coci. Yana daga cikin manyan fastoci a kasar nan da suka yi fice kuma suke da mabiya ba a Najeriya ba harda kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

Makon jana’izar faston zai fara ne da ranar 5 ga watan Yuli 2021.

Daga: Ahmad Aminu Kado.

One thought on “An nuna min marigayi Fasto TB Joshua na tiƙa rawa da Mala’iku a lahira a mafarki |– In ji Wani mabiyin sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *