An samu cigaba sosai a ɓangaren tsaro tun bayan dana hau mulki- In ji Buhari

An Samu Ci Gaba Sosai A Ɓangaren Tsaro— Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce a bayanan da yake samu daga hukumomin tsaro an samu ci gaba sosai a ɓangaren na tsaro, musamman bayan sauya shugabannin hukumomin.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya yi da shi.

“A Arewa Maso Yamma, ba shakka mun tura karin sojoji zuwa jihohin da suka fi fama da wannan matsalar, kamar a Zamfara, mun hana haƙar ma’adanai, su kansu ‘yan ƙasashen waje, mun hana su yin aiki a wannan waje, sannan ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen matsalar”, in ji shi.

“Matsalar Arewa Maso Yamma ita ce ta mutanen da ke da al’adu iri ɗaya suna kashe juna. Za mu tafiyar da su ta hanyar da suka fi fahimta. Mun bai wa ‘yan sanda da sojoji umarni da kada su raga musu. Idan aka kori mutane daga gonakinsu, za mu shiga cikin yunwa”, ya ƙara da haka.

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa: “A Arewa Maso Gabashin Najeriya, muna samun nasara a kan Boko Haram, kuma alamu na ƙara bayyana dake nuna cewa an kusa murƙushe su”.

Game da hare-haren ‘yan bindiga, Shugaban ya nuna damuwa a kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren ‘yan bindigar da ake zargin makiyaya ne, inda ya ce dole kowa ya yi mamaki a kan yadda makiyayan da a baya ake ganin su riƙe da sanduna a ce su ne a yanzu suke ɗauke da manyan makamai suna kashe mutane.

A cewarsa, rungumar shirin da gwamnatinsa ta ɓullo da shi na samar da matsuguni ga makiyaya zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar da ake fama da ita.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *