Ana ha’da baki da alkalai ana kwacewa Jama’a filaye a jihar Nasarawa ~Kungiyar kwadago

A wata fira da yayi da ‘yan jaridu wanda jaridar Mikiya ta samu fai-fan sautin muryar sakataren tsare-tsare na kungiyar kwadagon Nageriya NLC) Kwamrad Nasir Kabir ya nasafta dillalan fili dake jihar Nasarawa amatsayin barayin fili kuma Azzalumai dake satar filayen jama’a musamman filayen marayu wa’yanda iyayen su suka mutu, bayan samun wannan sautin muryar jaridar Mikiya ta tuntubi Kwamrad Nasir Kabir Kuma ya tabbatar da fitar maganar daga bakinsa ya Kuma bayyana mana cewa yayi wannan maganar ne biyo bayan Kara da wata mata ta kawo masa Kan yadda ake kokarin cinye mata filimta Mai girman filoti Goma dake Ruga ‘yar kasuwa a karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Kwamrad

Nasir Kabir ya Kara mana da cewa a yanzu haka suna shirye shiryen zanga-zanga matukar Gwamnatin jihar Nasarawa bata dauki mataki ga kawo karshen ire-iren wannan zalunci na kwacen filaye ba.

Kwamrad Nasir Kabir ya Kuma zargi wani Alkali Mai suna Mai Riga a fagen shiga da ha’da baki da dillalan filayen domin kwace filayen jama’a ya Kuma Kira sunan wasu dillalai biyu tare da shugaban su da yace sunyi kaurin suna wajen kwace filayen jama’a Kwamrad ya tabbatar Mana da cewa Sani Zangina shine shugaban dillalai masu kwacen filaye yayinda wani Alhaji Usman da Nasiru soja Suka kasance suna biye dashi a baya dukda Kwamrad ya tabbatar da cewa Alhaji Nasiru soja yanzu haka Yana tsare a gidan yari sakamakon wata shari’a da aka kashe jami’in dan Sanda dake da alaka da lamarin dillamcin filaye..

Har’ila yau Kwamrad Nasir Kabir ya ce a lakocin da Sanata Al’makura ke Gwamna a jiharta Nasarawa sun sha zama dashi domin bayyana Masa korafi Kan matsalar dillalan fili Amma ya gagara daukar mataki lamarin da yanzu haka ake kokarin ganin Gwamna A.A Sule na yanzu ya ɗauki matakin daya dace inji shi.

A takaice dai ga ka’dan daga sautin muryar firar da jaridar Mikiya ta tattauna da Kwamrad Nasir Kabir Kan wannan badakala da yace tana faruwa a jihar ta Nasarawa.👇

https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/11/Add-Music-To-Photo_Nov-28-080013-PM.mp4

Mun tuntubi Alhaji Sani zangina sai dai ya tabbatar mana da cewa ba zaiyi wata magana damu ba sai mun zo ofishin sa dake nan nyanya maraba…

https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/11/Add-Music-To-Photo_Nov-28-084951-PM.mp4
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *