Ana kashe mutane, an hana mutane walwala lallai Shugaba Buhari zai yi bayani gaban Allah |~ inji Tsohon Gwamna, Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan matsalar rashin tsaro.

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yace a halin yanzu yankin Arewa maso yamma yana cikin masifa.

Babban ‘dan siyasar ya koka kan halin da mutanen yankin na sa da na shugaban kasa ke ciki.

“Sha’anin rashin tsaro wani bala’i ne da ya auko mana. Mutanen da ke can ne kurum za su iya bayanin halin da ake ciki a Sokoto da Zamfara.” – Bafarawa.

“Abin

takaicin shi ne tsaron kasa na kan wuyan gwamnatin tarayya ne.

Masu fadawa Buhari abubuwa suna tafiya daidai (ko suna ce masa da matsala ne?).”

“Idan suna fada masa abubuwa suna tafiya daidai ne, sun cuce sa, kuma sun cuce mu.”

Attahiru Dalhatu Bafarawa yake cewa Allah (SWT) ya san cewa ana cikin mummunan yanayi a yankinsa na Arewa maso yamma, domin mutane suna kuka.

“Yau, na je gida na dawo, na shaida da idanuna (ba fada mani aka yi ba). Mutane sun noma shinkafa da gero, amma ba za su iya kai amfaninsu gida ba.”

“Duk wanda ya je gona ya dauko kayan noman da ya samu, ba zai dawo da rai ba. A irinsu Zamfara, an tsare mutane, babu waya, kuma an rufe kasuwa.” Da aka tambayi Bafarawa ko adawa ce ta sa shi yake irin wadannan maganganu, sai yace lamarin ya shafi har shugaban kasa, kuma Allah (SWT) zai tambaye shi.

Daga Ahmad Aminu kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *