Ba gaskiya bane bance Ina son Pantami ba ~Cewar Jaruma Hadiza Gabon.

A ƴan kwanakin nan wani labari yayi ta yawo a kafar sada zumunta cewa Hadiza Gabon ta sha alwashin sai ta zamo matar Sheikh Isah Ali Pantami wanda wannan labarin ya ɗauki hankali sosai a kafar sada zumunta musamman ta facebook.

To sai dai Jaridar Idon Mikiya, tayi wani bincike kan wannan maganar, inda ta gano wani mabiyin jarumar a kafar Instagram bayan ta wallafa wani gajeren bidiyo daga Tiktok tana rera wakar wani mawakin turanci sai yayi mata tambaya kamar haka.

@sadiqgidado

“Hajiya Hadiza Gabon dan Allah mene gaskiyar maganar da ke ta yawo a Social Media, cewar kina matukar son Minister Pantami, har ma kina iya barin sana’ar film idan zai aure ki?”

@adizatou “Ba gaskiya ba ne ba.” Inji ta

Sai wani shima da yayi masa tasa tambayar kamar haka:

@mujee_0 “A yanzu nan na karanta wani labarin jita jita cewa babban burin ki a rayuwa ki auri Prof. Isah Ali Pantami.”

@adizatou “Ba gaskiya ba ne.”

daga Idon Mikiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *