Ba zai yiwu kasarmu ta dogara kan sojoji ba kadai, sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba|~ Inji Tukur Buratai

Tukur Buratai, jakadan Najeriya a jumhuriyar Benin ya ce ba zai yiwu kasar ta dogara kan sojoji ba kadai don magance matsalolin tsaro.

Buratai ya kuma ce akwai bukatar samun ci gaba a arewa maso gabas don magance lamarin ta’addanci a yankin.

Tsohon shugaban hafsan sojin kasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 22 ga watan Oktoba, a wajen wani taro a garin Yola.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *