Ba zan iya kai ziyarar Jaje ga Jihohin da Suka samu hare-haren ta’addanci ba ~Cewar Shugaba Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bakin Ministan ‘yan Sanda ya kare kansa Kan rashin zuwansa sokoto Bayan ‘yan Bindiga sun kone matafiya kurmus a Lokacin da yake amsa tambayoyi Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, ya ce a zahiri ba zai taba yiwuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje ga jihohi da iyalan da rashin tsaro ya shafa ba.

An dai yi ta cece-ku-ce kan rashin zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihohin da aka samu manyan hare-hare.

Kwanan

nan, kasancewar shugaban kasar a wajen kaddamar da littafi sa’o’i bayan da ‘yan bindiga suka kona wasu fasinjoji da ransu a Sokoto, ya haifar da martani.

Duk da cewa daga baya Buhari ya aike da wata tawaga mai karfi zuwa jihohin Sokoto da Katsina, inda aka samu tashin hankali, amma har yanzu masu suka na ganin rashin zuwansa amatsayin wani Babban Laifi.

Dingyadi ya ce hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’addan ke kai wa ba su kau da kai ba ya sa shugaban ya ziyarci dukkan wuraren.
Sai dai a wata hira da BBC Hausa, ministan ya ce ba zai yiwu Buhari ba, a matsayinsa na shugaban kasa ya ziyarci dukkan wuraren saboda yanayin aikinsa da kuma abubuwan da suka faru.

“Wadannan hare-haren suna faruwa kusan a kullum kuma ba zai yiwu shugaban kasa ya ziyarci dukkan wuraren domin jaje ba. Kuma idan ka aika tawaga, kamar kana can, duk daya ne,” inji shi.

Ministan ya kuma ce, jami’an tsaro a kasar nan suna aiki tukuru domin dakile ayyukan ‘yan bindiga.

A nasa martani, dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza ya ce tura tawaga ba abin da suke so daga shugaban kasa ba ne, a’a suna son daukar matakin da zai kawo karshen ayyukan ‘yan fashi a jihar.

“Tabbas tawagar shugaba Buhari sun zo sun same mu, amma ba abin da muke so ba kenan. Abin da muke so a halin yanzu shine aiki. A karamar hukumar an kashe daruruwan mutane amma duk da haka gwamnatin tarayya ba ta dauki wani mataki ba.”

Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan Sokoto, ya yi zargin cewa shugaban kasar bai ziyarci jihar ba saboda rayuwar al’ummar kasar ba ta da nasaba da shi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *