Ba zan iya tona Asirin masu daukar nauyin ‘yan ta’addan Boko Haram a idon Jama’a ba~cewar Shugaban EFCC Abdulrashid bawa.

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, a ranar Alhamis, ya ce ba zai iya fitowa fili ya ambaci wadanda ke tallafawa Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci a Najeriya ba.

A farkon makon, mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa sun lissafa ‘yan Najeriya shida cikin wadanda ke tallafa wa ta’addanci. Sai dai Da aka tambaye shi game da wadanda ke tallafa wa ta’addancin a Najeriya a gidan talabijin na Channels, Mista Bawa ya ce ba zai iya tattauna batun tsaro na kasa mai mahimmanci a gidan talabijin na kasa ba.

Mai

Yana Mai Cewa “Idan kai ne mai ba ni shawara za ka ba ni shawara in zo gidan talabijin na kasa don fada wa duniya baki daya game da batutuwan da suka shafi tsaron kasa?”, In ji Mista bawa Amma abin da nake so in tabbatar muku muna aiki ba tare da gajiyawa ba tare da sauran hukumomin ‘yan uwa don tabbatar da cewa kasar ta kubuta daga ta’addanci.”

Idan baku manta ba Gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin wallafa sunayen wadanda ke tallafa wa ayyukan ta’addanci a kasar. Amma zuwa Yanzu dai Basu cika Alkawari ba. Rahotan people Gazzete.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *