Babu Ruwan Ki da Kawaye Ki Fita Harkar su Gaba Ɗaya — Wata Matashiya Taji Iyayen Amarya Na Faɗawa Ƴarsu Bayan Ta Sayi Tikitin Jirgin Sama Domin Halartar Bikin.

Wata matashiya mai suna Maryam Muhammad ta haɗu da abinda ya daɗe yana faruwa a ƙasar Hausa, idan za’a kai amarya ɗakin mijin ta.

Matashiyar, kamar yadda ta wallafa a shafin sada zumunta na Facebook dinta, ta bayyana yadda iyayen ƙawarta suka harzuƙa ta, har takejin dama bata yi hidimar siyan tikitin jirgin sama ba, da kashe kuɗi wajen kwalliya domin halartar bikin.

Matashiya

Maryam Muhammad, tace ba zata taɓa mantawa da abin ba, duba da yadda tayi hidima domin ganin ta halarci bikin.

Ga kalaman ta:

Salamu Alaikum Friends Zo kuji wani abin haushin da ya faru damu Wanda bazan taba mantawa dashi ba,

Shi dai wannam kwalliyar da kuke gani wlh kudi da yawa na biya aka yi min Saboda Marriage na wata Friend ina, Yau kusan week kenan ina bin auren a raina toh auren ba agarin mu bane wani gari ne daban amma bazan fadi ko ina ba,

Maryam Muhammad tace dakyar ta samu ta lallaɓi iyayenta suka barta ta tafi bikin, tare da siyan tikitin jirgin sama, baya ga yin kwalliya mai ɗan karen tsada.

Kamar yadda take cewa:

“Da kyar na lallaɓi Dad da Mom akan su barni naje wannan auren haka a kabani kudi na siya Ticket nabi Plane, Munyi hidima sosai a bikin amma babban abin bakin cikin shine duk da irin yadda mu kayi ba’agani ba, Da akazo kai Bride (amarya) Gidan ta sai ji mu kayi ana cewa babu Ruwan ki da Kawaye ki fita a harkar su nan gaba.

Maryam Muhammad ta ƙarƙare rubutun ta tambayar wai daman haka ake yiwa amare ko kuwa raina su akayi?

Ga Maryama:

Please dama haka akeyi ne ko kuma saboda kawai raina mu akayi ne aka faɗa mana haka“.

Mafi akasari dai, iyaye mata kan yiwa amarya faɗa da nasiha a matsayin su na waɗanda suka ga jiya suka ga yau.

To amma dai ga Maryam, haƙiƙa wannan abu yazo mata a matsayin wani abu baƙo wanda bai mata daɗi ba.

Shin a ganin ku hakan da sukayi iyayen yarinyar sun kyauta ko kuwa basu kyauta ba?

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *