Babu wanda nake so da zan goyawa baya ya zama shugaban kasa a Zaben 2023 ~Cewar Shugaba buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ranar Laraba ya ce bai damu da wanda zai gaje shi ba, yana mai jaddada cewa 2023 ba matsalarsa ba ce.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Channels TV.

Wannan ikirari nasa ya sha banban da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da yayi kokarin ganin marigayi shugaba Umaru Musa Yar’adua ya gaje shi a shekarar 2007 a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugaba Buhari, wanda aka tambaya kan ya ce wani abu game da zaben 2023, ya ce: “2023 ba matsalata ba ce, ban damu da wanda zai gaje ni ba, a bar mutum ya zo, ko wane ne ba ruwa na.

“Dukkan

abubuwan da ke da mahimmanci na tabbatar da cewa na rubuta. Kada wani ya ce in zo in ba da wata shaida a kotu bayan na Gama mulki,

“Ba ni da wanda na fi so a 2023 a jam’iyyata, ba zan yi haka ba saboda za a cire shi kafin in ambata, zai fi kyau in boye shi.”

Shugaban ya ce: “Abin da na gada shi ne, zan yi kokarin ganin mun gudanar da ayyukanmu cikin gaskiya, wanda ke nufin mun dakatar da duk wani sata gwargwadon yadda ikon da zan iya ba da izini. Za mu hana almubazzaranci ga ’yan Najeriya wanda hakan na da matukar muhimmanci.”

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *