Babu Wata Jiha Da Take Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Nijeriya Kamar Kano, In Ji Ganduje.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce babu wata jiha da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya sama da jiharsa, kasancewar ita kadai ce a duk fadin tarayyar Najeriya take da wata hukuma mai yaki da cin hanci da rashawa da ke rage matsalar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin ranar Ombudsman ta Duniya da aka gudanar a Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano (KANCI) a Kano.

Ganduje wanda ya samu wakilcin Babban Lauyan Gwamnatin kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Lawan Musa Abdullahi, Ganduje ya ce tare da kafa Hukumar Korafin Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar (PCACC) da Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, jihar ta ba da hadin kai ga kokarin Gwamnatin tarayya wajen kafa yaki da cin hanci da rashawa.

A

nashi bangaren, Shugaban zartarwa na hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce dokar da ta kafa hukumar ta samar mata da ikon ta na farar hula da na masu aikata laifi.

Ya ce a karkashin sashe na 9 na dokar hukumar, PCACC na da ‘yancin tabbatar da cewa babu wani dan asalin jihar Kano da aka yaudara.

Wakilan EFCC, ICPC da NHRC duk sun yaba wa kokarin hukumar kan hadin kan da take yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda suka kara da cewa hukumar ta tabbatar da kimarta a tsawon shekarun da aka kafata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *