Bai kamata ‘yan bindiga su yi tunanin banza suke ci ba, tabbas na sha alwashin cewa gwamnatina ba zata bar wasu tsiraru su hana ‘yan Najeriya zaman lafiya ba, |~ Inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya yi kakkausan gargaɗi kan yan bindiga bayan kashe mutum 15 a kananan hukumomin jihar Sokoto.

Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba zata bar wasu tsiraru su hana yan Najeriya zaman lafiya ba.

Yace gwamnatinsa zata cigaba da samar wa jami’an soji kayan aiki domin su kawo karshen waɗan nan tsagerun baki ɗaya.

Daga Ahmad Aminu kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *