Bani ‘dauke da Juna Biyu ~Cewar Aisha Buhari

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bayyana Cewa Bata dauke da juna biyu sabanin labaran da ake yadawa a shafukan intanet na Najeriya kwanan nan Mrs Buhari ta bayyana hakan ne ta bakin mataimakin ta a zantawarsu da BBC Pidgin.

An rika yada jita-jitar cewa matar shugaban kasar na dauke da juna biyu bayan dawowarta gida Najeriya a tafiyarsu zuwa kasar Turkiyya tare da mijinta.

A wata hira da BBC Pidgin, mai taimaka wa Mrs Buhari, Sulaiman Haruna, ya ce Aisha Buhari tana da kirki.

Wasu

kafafen yada labarai na yanar gizo sun ruwaito cewa ta kamu da wata cuta da ba a tantance ba wacce ke nuna cikinta a matsayin mai ciki.

Haruna ya ce rahotannin Wasu na cewa Uwargidan Buhari na fama da ciwon daji ko ciki Wanda wannan ba komai ba ne illa shirme kawai.
“Zan iya Tabbatar maku kashi 100 cikin 100 cewa Uwargidanmu na da cikakkiyar lafiya kuma ba ta da ciki kamar yadda wasu suka ruwaito.

“Wasu daga cikin waɗannan rahotannin daga masu yada jita-jita ne waɗanda ba su da tushe balle ma’ana mai kyau.

“Ku sani a wannan zamanin na yau, mutane na iya sarrafa hotuna,” in ji shi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *