Basusukan da kasashen Afirika suke ciyowa ba a yin ayyukan da suka dace da su – Cewar Shugaba Buhari.

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce basussukan da kasashen Afirka suka ciwo kafin soke su na kasashe 32 a shekarar 2005 ba a saka su cikin kayayyakin da suka dace na tattalin arziki da ayyukan da za su iya kawo ci gaban da ake bukata ba.

Ya fadi haka ne a wajen taron baje kolin wani littafi kan Ambasada Bamanga Tukur mai suna “Legacies of a Legend”.

Buhari,

ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari, wanda shi ne ya jagoranci bikin. Ya ce karbo basussuka, idan har an yi yarjejeniya da su yadda ya kamata kuma aka yi amfani da su yadda ya kamata, wani muhimmin makami ne a tsarin tattalin arziki na gwamnati a fagen siyasarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *