Bayan mun cire tallafin mai Zamu rinka tallafawa talakawa da naira dubu Biyar Biyar N5,000 duk wata ~Cewar Gwamnatin Shugaba Buhari.

A wani taro data halarta Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta ce ‘yan Najeriya za su samu Naira 5,000 duk wata a matsayin tallafin sufurin zirga-zirga bayan an cire tallafin mai

A cewar Ministan, Gwamnatin Tarayya za ta cire tallafin man fetur nan da shekarar 2022 Mai zuwa tare da baiwa talakawan Najeriya tallafin sufuri na Naira 5,000.

Ministar ta bayyana haka ne a yau ranar Talata, a wajen taron kaddamar da wani rahoto na bunkasa ci gaban bankin duniya a Abuja, inda ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 30 zuwa 40 ne wadanda suka fi fama da talauci a kasar, za su samu tallafin.

“Kafin

tsakiyar shekarar 2022 da aka yi niyya kawar da tallafin mai gaba daya, muna aiki tare da abokan aikinmu kan matakan dakile illar da ke tattare da kawar da tallafin ga masu rauni a kasa kashi 40% na al’ummar kasar. .

“Daya daga cikin irin wadannan matakan shi ne kafa tallafin sufuri na wata-wata a matsayin mika kudi daga Naira 5,000 zuwa tsakanin Mutane miliyan 30 zuwa 40 wadanda suka cancanta ‘yan Najeriya.”

Mrs Ahmed ta kuma bayyana fatan cewa dokar masana’antar man fetur ta 2021, da sake farfado da matatun mai, da kuma bude wasu matatun mai masu zaman kansu guda uku a shekarar 2022 za su bunkasa tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *