Bayan shekaru bakwai da gudowa daga komar ƴan Boko Haram, ɗalibar ta samu nasarar kammala digirin ta a jami’ar Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ne ya sanar da labarin mai daɗin ji ta shafin sa na Facebook a yau asabar.

Yarinyar mai suna Mary Katambi, ta zamto ta farko a cikin jerin waɗannan yan mata data fara zama mai riƙe da digiri, tun bayan da Bokoharam ta sace su a Shekarar 2014 daga makarantar Chibok.

Yanzu kenan, Katambi ta zama tana da ƙwarewa a fannin aikin banki daga jami’ar ilmi ta Amerika dake Yolan Adamawa.

A cewar Atiku Abubakar cikin harshen Ingilishi ya faɗa cewar:

“Yake Mary Katambi, haƙika ina matuƙar alfahari dake, sakamakon samun nasarar ficewa daga duk wani ƙalubale na rayuwar ki, musamman ma guduwa daga hannun ƴan Boko Haram, sannan kika zama mai digiri a ɓangaren banki a wannan jami’a ta Amerika dake Najeriya. Shekaru masu tarin albarka na jiranki a rayuwar ki wacce bata zo ba”.

Sannan Atiku Abubakar ya turo hotunan sa da yarinyar cikin matukar jin dadi da annushuwa.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *