Bikin Sallah: idan mukayi dauriya zamu samu Matsayin mafi girma a wajen Allah ~Inji Sanata Uba Sani.

A Lokacin da yake aikewa da sakon barka da Sallah acikin wata sanarwa Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya malam Uba Sani Yana cewa.
A Tare da gaisuwar ban girma ga musulmin da ke gida Najeriya da ma duniya baki daya a kan bukukuwa na musamman na farin ciki bisa zuwan sallar Eid-el-Kabir. Wanda aka fi sani da “Bikin Hadaya”, wannan bikin yana girmama yardar Annabi Ibrahim (AS) na sadaukar da dansa, Isma’il a matsayin biyayya ga umurnin Allah Maɗaukaki ya ba shi lada mai yawa bisa haka.

Sanatan yayi addu’a inda yace Wannan yana koya mana cewa sadaukarwa ta gaskiya duk da cewa Yayin sadaukarwa, ana iya yi mana izgili, wulakanci da ba’a. Amma idan muka kasance ba tare da tsoro ba, muka mai da hankali da kuma ƙarfin hali, hakika wannan sadaukarwa tamu za ta kasance mai amfani kuma za a ɗaukaka mu zuwa matsayi mafi girma. Allah zai bamu lada mai yawa. ‘Yan uwanmu maza da mata za mu kasance cikin wani sabon yanayi. Wahalarmu za ta wuce Kamar yadda yake da alaƙarmu da Allah, haka ma yake da matsaloli da ƙalubalen da muke fuskanta a cikin al’ummominmu a yau saboda rashin tsaro.

Duk da irin kalubalen da muke fuskanta har yanzu muna rike da imaninmu da dogaro ga Allah Madaukaki. Allah yana ganin zukatanmu kuma ba zai taba barinmu ba. A ƙarshe zai taɓa zuciyar miyagu kuma ya kawo canji ga ayyukansu. Idan sun kasance masu taurin zuciya, zai sanya su a wuraren da suka dace. Da za su sake samun zaman lafiya.

Na sadaukar da wannan sakon na Sallah ga mutanena na fama da doguwar wahala na shiyyar Kaduna ta Tsakiya. ‘Yan fashi, masu satar mutane da sauran masu aikata laifuka sun kewaye yankinmu mai muhimmanci da Rashin tsaro ya ci gaba da lalata nasarorin da muka samu ta fuskokin tattalin arziki da ilimi. Mutanenmu suna tsoron makomarsu. Akwai tsoro mai firgitarwa, damuwa Amma ba halin rashin kauna bane domin Hukumomi suna gaba gaba a hankali suna magance matsalar rashin tsaro. Gwamna Nasir El-Rufai da hukumomin tsaro suna aiki kai tsaye don ganin an shawo kan lamarin. Ina tabbatar wa masoya na cewa sakamakon wannan kokarin zai bayyana nan ba da dadewa ba.

Ina kira ga jama’ata da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai. Ku shirya kanku a matakin al’umma ku sanya ƙungiyoyin sa ido don tattara bayanan sirri da faɗakarwa cikin hanzari bari mu karfafa mutanen mu Kan su ci gaba da jajircewa kuma su ci gaba da nuna karfin gwiwa yayin fuskantar kalubalen. Dole ne mu zama masu addu’a. Idan munyi riko da Allah, zai sanya mana hanya. Lokutan marasa kyau ba zasu Dore ba ba. Hakika Mutanenmu za su kasance a yanayin murmushi.

IDI MUBARAK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *