Boko Haram ta kwace kauyaku biyar a jihar Niger bayan Gwamnatin jihar ta Kashe Bilyan biyu 2bn a harkokin tsaro.

‘Yan ta’addar Boko Haram sun kwace garuruwa biyar a kananan hukumomin Rafi da Shiroto a jihar Neja, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Matane ya bayyana.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a Minna, babban birnin jihar a ranar Litinin.

Ya yi bayanin cewa mayakan na Boko Haram suna da cikakken iko a kauyakun Hanawanka, Madaka, a karamar hukumar Rafi da Kurebe, Gussau, Farina Kuka a karamar hukumar Shiroro, lamarin da ya tilasta wa mazauna karkara yin hijira zuwa wasu wurare masu aminci.

Ya

ce ‘yan ta’addan na tafiya cikin walwala a yankunan da abin ya shafa, suna rike da nagartattun makamai da kuma muggan makamai.

ya ce tuni jihar ta sanar da hukumomin tsaro domin daukar matakan tsaro na gaggawa.

“Mun kashe sama da Naira biliyan 2 kan jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a cikin shekaru biyu da suka wuce.

Za mu ci gaba da ba da fifiko ga jin dadin jami’an tsaro da aka tura domin ba su damar kawar da duk wadanda ke da hannu a cikin haramtattun ayyuka na zaman lafiya, ci gaba da kwanciyar hankali na siyasa.

“Hakazalika, mun yi kira ga mazauna yankin da su ba da gudummawar ingantattun bayanai game da zirga-zirgar miyagun halaye zuwa ga Jami’an tsaro mafi kusa don daukar matakan tsaro.

“Mun kuma tuntubi shugabannin gargajiya da na addini da kuma masu ruwa da tsaki don jawo hankalin jama’a domin tallafa wa kokarin gwamnati a ci gaba da yaki da masu aikata laifukan” inji shi.

ya kuma yaba tare da yabawa kokarin gwamnatin jihar Neja na shawo kan matsalar.

Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawo karshen kalubalen tsaro da ke addabar jihar. (NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *