Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, |~ Inji Masari

Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya ce gwamnatin Buhari ta kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar jama’ar Katsina.

Gwamnan ya ce gwamnatin Buhari ce ta farko da ta fara kai wa gidaje masu fama da matsanancin talauci tallafi a arewa.

Masari ya sha alwashin biyan dukkan kudaden fansho da na garatuti da ake bin gwamnatin jihar Katsina kafin cikar wa’adin mulkinsa.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *