CHRISTMAS: Idan muka cire bam-bamce Bam-bamce Zamu iya kawo karshen ta’addancin Nageriya ~Cewar Sanata Uba Sani.

A nasa Sakon taya murna ga bikin Murnar ragayowar Ranar kirsimeti Sanata Uba Sani ‘dan majalisar dattijan Nageriya dake wakiltar Yankin kaduna ta yayi Kira ga zaman lafiya a Nageriya Sanata na Cewa Barka da Kirsimeti, zuwa ga ’yan’uwanmu Kiristoci masoya. Muna godiya ga Allah madaukakin sarki daya bamu ikon ganin wannan Rana ta farin ciki. Da fatan wannan lokacin ya kusantar da jama’armu da kuma taimaka wa kasarmu da ke cikin mawuyacin hali.

Ana bikin wannan Kirsimeti ne sau Daya cikin shekarar wanda ba za mu manta cikin gaggawa ba Acikin wannan Shekara ce mafi ƙalubale Tun daga batun tattalin arziki zuwa tsaro da rayuwa, Wanda ya kasance labarin zafi damuwa da fargaba. Amma abin da ya fi daukar hankali shi ne munanan ayyukan ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka. Sun dade suna rike da al’ummarmu don neman fansa. Sun lalata tattalin arziƙin cikin gida tare da mayar da Wasu yankuna kufai.

A

wasu al’ummomi, rashin haɗin kai yana hana ɗaukar matakan da Suka dace kan masu aikata laifuka Dole ne mu gane cewa ayyukan masu aikata laifuka suna barazana ga ko wanne bil’adama. Dole ne mu koyi sarrafa bambance-bambancenmu kuma mu hada kai don fuskantar babbar barazana ga rayuwarmu baki daya. Wannan lokaci ne dake ba mu dama ta musamman don yin sulhu da juna. Yesu Kristi a hidimarsa a duniya ya yi wa’azin ƙauna, sulhu, gafara da salama. Mu yi koyi da nagarta ta sulhu domin a warkar da kasarmu da ke cikin mawuyacin hali. Dole ne mu yi sulhu da ƴan ƙasa, kuma mafi mahimmanci, da Allah. Idan muka yi abubuwan da ke faranta wa Allah rai, za mu shawo kan matsalolinmu kuma al’ummarmu za su ji daɗin zaman lafiya.

Ina so in yi amfani da wannan damar, in sake yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki tsattsauran mataki a kan ‘yan ta’adda, ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka da ke sa rayuwa kunci ga al’ummarmu. A kullum sai kara jajircewa suke yi, kuma idan ba a kula ba Hakan na iya yin barazana ga zaman lafiyar al’ummar Najeriya.

Ina mika sakon taya murna ga masoyana, al’ummar mazabar Kaduna ta tsakiya kan wannan gagarumin biki. Kun sha wahala sosai a wannan shekara. Masu aikata laifuka sun yiwa al’ummarmu kawanya. Shiyyarmu ta cancanci kulawa ta musamman daga Gwamnatin Tarayya. Dole ne hukumomin tsaro su gudanar da ayyuka na musamman a kananan hukumominmu da ke fama da tashin hankali kamar Birnin Gwari, Giwa, Kajuru, Igabi da Chikun domin kawo karshen wannan Matsala Inji Sanatan

Sanatan ya Kuma rufe da jinjina ga Al’ummar da yake wakilta Yana Mai Cewa Ubangiji ya ci gaba da tsarewa da karfafawa al’ummar shiyyar Sanatan Kaduna ta tsakiya masu hazaka da juriya. Ya saka muku kan sadaukarwar ku Zuwa ga alkhari.

BARKANMU DA KIRSIMETI!!!

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *