CIGABA YAZO: Za’a soma gudanar da shari’ar masu laifuka ta yanar gizo-gizo a Najeriya.

A farkon makon nan ne Ministan Shari’a na ƙasar nan wato Abubakar Malami, ya sanya wa wannan dokar hannu, inda ake sa rai, dokar zata don aiki nan take.

Shugaban hukumar kula da gidajen yari na ƙasar nan, Rauf Aregbesola yayi maraba da wannan doka inda yace, daga cikin 68,000 na ɗaurarrun dake cikin gidajen gyaran hali na ƙasar nan, guda dubu goma sha bakwai ne aka samu damar yanke musu hukunci.

Shugaban hukumar yace, yanke wannan hukunci, zaisa a rage yawan cinkuson dake gidan gyaran hali, tare da rage yawan masu jira a yanke musu hukunci a gidajen yarin ƙasar nan.

class="wp-block-image size-full">

DSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, shine jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano, ya tabbatar da cewa wannan doka zata taimaka wajen gudanar da shari’a cikin sauƙi, sannan yawan cinkuso zai ragu. A cewar sa:

“Wanann sabon tsari da Ministan Shari’a ya kawo, tsari ne mai kyau zai rage cinkuso, in muka kalla misali, ƙasashen duniya sun hau kan tsarin sosai, kuma akan sa suke”.

To sai dai ba anan gizo ke saka ba, domin masana Shari’a sunce dokar nada nata kalubalen.

Ƙalubalen kuwa sune:

1) Najeriya na matsalar sabis ɗin intanet (yanar gizo-gizo)

2) Sai kuma matsalar wuta.Inda suka ce , indai za’a magance wannan matsalar, to tabbas tsarine mai kyau a lokacin da ake ƙoƙarin ganin an rage cinkoson al’umma a waje guda saboda Corona virus.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *