Cigiyar wani Matashi mai suna Usaini Skipper daya ɓata ba’a san inda ya shiga ba, a ƙalla sati ɗaya kenan.

Shi dai wannan matashin sunan sa, Usaini Tanko, wanda akafi sani da suna Usaini Skipper. Mazauni ne a garin ƙiru dake Kano.

Kimanin satinsa guda da yayi batan dabo, ba’a san inda yayi ba, hakan ne yasa hankalin yan uwa da abokan arziki yayi matuƙar tashi. Saboda Usaini mutumin kirki ne, kuma mutum na kowa. Samun abokin faɗan sa, abune mai wuya gida da waje.

Rahotanni

sun nuna Usaini Tanko ya fita daga cikin gidansa da misalin ƙarfe 3:00 na dare wanda har kawo iyanzu ba’a same shi ba, ba’a san inda ya shiga ba.Ana barar adu’arku ubangiji Allah ya bayyana shi.

Idan kuma an Usaini ɗan Allah a taimaka a kaisa ofishin yan sanda ko wata hukuma mafi kusa ko gidan radio ko a tuntubi wannan lambobin waya:

08067295669,

08038999292,

08033079653,

07087204440,

08086018988,

Allah yasa a dace.

Ameen.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *