Cikin Shekaru shida na mulkina ‘yan Nageriya sun tabbatar da cigaban ababen more rayuwa da muka samar a gare su~Cewar Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya ce ‘yan Najeriya za su iya kula da kansu idan aka samar da ababen more rayuwa.

Buhari ya bayyana haka ne a yau ranar Alhamis a yayin ganawarsa da shugaban bankin raya Musulunci, Mohammed Al-Jasser, a wajen taron zaman lafiya na birnin Paris a kasar Faransa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken ‘Idan aka samar da ababen more rayuwa ga jama’ar mu za su iya kula da kawunansu, in ji shugaba Buhari ga shugaban IDB.

A

cewar sanarwar, Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin an sake farfado da ababen more rayuwa ga Najeriya domin dorewa.

“Muna kokawa sosai kan ababen more rayuwa saboda ba za a iya samun ci gaba mai dorewa ba tare da shi ba,” in ji shugaban

Ya ci gaba da cewa, “Bisa la’akari da fadin kasarmu, muna bukatar tituna, layin dogo, wutar lantarki, filayen jirgin sama, gidaje, abin da muka tsunduma kanmu kenan cikin shekaru shida da suka gabata. Kuma mutanenmu suna ganin sabbin abubuwan da ke faruwa. Dangane da albarkatun da muke da su, ba mu yi mummunan aiki ba. Lokacin da aka samar da ababen more rayuwa, mutanenmu za su iya kula da kansu.”

Da yake godiya ga shugaban IDB, Buhari ya ce, “Abin da muka dogara da shi (danyen man fetur) munyi hasarar makamashi mai yawa amma Yana dawowa a hankali, Muna Kan kokarin haka Amma muna sa ran babban hadin kai daga gare ku.

Da yake mayar da martani, Al-Jasser ya shaida wa Buhari cewa, “Na gamsu da manufofinka na samar da ababen more rayuwa, wadanda za su ba wa matasa dama, da karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu. Najeriya kasa ce mai muhimmanci a gare mu, kuma ta cancanci duk taimakon da za ta iya samu.”

Daga nan sai shugaban na IDB ya tabbatar wa Buhari cewa bankin zai ci gaba da tallafa wa Najeriya, saboda babban aikin sa shi ne inganta ci gaba a tsakanin masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *