DA ƊUMI-ƊUMINSA: An garzaya da Sunday Igboho asibiti daga Kurkuku, ya kamu da matsananciyar cutar Koda

An garzaya da mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo wanda akafi sani da Sunday Igboho asibiti bayan kamuwa da cutar koda da yayi a Kurkukun Kotonou.

Daya daga cikin Lauyoyinsa, Yomi Aliyu, ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi.

A cewar, Sunday Igboho na fama da matsanancin rashin lafiya kuma an garzaya da shi asibiti.

Yomi Aliyu yace: “Igboho bai kamu da cutar nan kafin tsareshi a Kotono ba. Abin yayi muni da ya kai sai da aka garzaya da shi asibiti.”

“Ban

sani ko yanzu sun mayar da shi Kurkuku daga asibiti ba, amma yana fama da matsanancin rashin lafiya kuma da alamun abin ya shafi kodarsa da huhunsa.”

Wasu daga cikin kungiyar Ilana Omo Oodua sun tabbatar rashin lafiyar Igboho.

Wani ya bayyanawa Punch cewa: “Lallai yana fama da rashin lafiya kuma da alamun ya shafi kodarsa. Bamu tabbatar ba tukun don sai an sake gwaji.

Muna kokarin ganin cewa yana samun kula mai kyau.”

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *