Da ɗumi-ɗuminsa: An ware Biliyan N100 domin gudanar da zaben 2023, kudin sunyi kaɗan |~ Cewar Shugaban INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ta ce naira biliyan 100 da aka ware domin gudanar da babban zaben 2023 a kasafin kudin sabuwar shekara ba zai isa ba ko kadan.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a yau Juma’a, yayin da yake kare kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin majalisar dattawa.

Ya ce a babban zaben 2019, naira biliyan 189 aka ware don haka babu yadda za a na zaben 2023 yayi kasa.

Daga

Ahmad Aminu kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *