Da Ɗumi-Ɗuminsa: Buhari ya samu lambar yabo daga kasar Ingila ta shugaban da ya gina Najeriya da kamanta Adalci

An bai wa Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) lambar yabo ta shugaban da ya gina kasa a wani taron da Jam’iyyar APC, reshen Ingila ta shirya, don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai a London.

Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Jacob Ogunseye, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikewa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba a Abuja.

Ya ce an kuma zabi Jagoran Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu don bashi lambar yabo ta Shugabanci a taron da aka yi ranar 2 ga Oktoba, a Dorchester Hotel da ke Landan a kasar Ingila.

A

cewar sanarwar, duk da kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu, makomarta tana da haske mai gamsarwa, ta kara da cewa ya kamata a dauki ranar ‘yancin kai a matsayin ranar tunawa kan abubuwan da suka gabata na kasar, yin aiki akan halin da ake ciki da tsara makoma.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *