Da ‘dumi ‘dumi A Sokoto ‘yan Bindiga sun sake sace mutun Sha ‘daya 11ciki harda Limamin juma’a

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da babban limami, Aminu Garba, da ke shirin gabatar da sallar Juma’a a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.

A ranar Juma’a ne aka yi garkuwa da Imam tare da wasu mutane uku.

Maharan sun kuma tare hanyar Sabon Birni zuwa Gatawa a ranar Asabar, inda suka harbe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu bakwai.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Sa’idu Ibrahim, wanda ya tabbatar da harin, ya ce wadanda suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawa a wani asibiti da ke Wamakko.

Ya

ce wata mata da aka harbe a kauyen Dama ta yanke kafarta saboda ba a iya gyara ta.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya ce zai tuntubi jami’in da ke kula da yankin ya koma ga wakilinmu amma bai yi hakan ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *