DA DUMI DUMI: An Kama Kirista A Sahun Gaba A Wani Masallacin Juma’a A Kaduna.

An kama Kirista a sahun gaba a wani Masallaci Juma’a a Kaduna.

Rahotanni daga masallacin juma’a na Kauri dake karamar hukumar Kaduna ta kudu na cewa an kama wani Kirista ya yi shigar burtu a sahun gaba na masallacin a lokkacin da ake gudanar da sallar juma’a.

Mutumin mai suna John Danjuma ya shiga sallar juma’a ne, sai daga baya aka gane shi Kirista ne Wanda kawo yanzu ba a san dalilinsa na yin hakan ba.

A halin yanzu an mika shi ga kungiyar ‘yan banga na yankin don cigaba da bincike da daukar mataki.

wannan

bawan Allah ya Shiga masallacin ya yi Sallah, bayan an idar da Sallar kuma ya cigaba da bara tare da rokon kudi a masallacin.

Malam Musa Yahaya Hamza, daya daga cikin wakilan Masallacin ne ya bayyanawa Jaridar Mikiya wannan labari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *